1 Ana nufin, magaji, muddin yana yaro bai fi bawa ba, ko da yake yana da mallakar dukkan kome.
2 A hannun iyayen goyo da wakilai yake har zuwa ranar da mahaifinsa ya sa.
3 Haka yake a gare mu, wato sa'ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al'adun duniya muke.
4 Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a,
5 domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari'a, a mai da mu a matsayin 'ya'yan Allah.
6 Tun da yake ku 'ya'ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, yana kira, “Ya Abba! Uba!”