11 sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa.
12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!”
13 Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah.
14 Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.”
15 Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi banruwa ran Asabar?
16 Ashe, bai kamata matar nan 'yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?”
17 Da ya faɗi haka, sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwan al'ajabi da yake yi.