20 Sa'an nan ya yi addu'a da gaske ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wa gwauruwan nan da nake zaune wurinta masifa, ka aukar wa ɗanta da ajali?”
21 Sa'an nan ya kwanta ya miƙe a kan yaron sau uku, ya kuma yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka sa ran yaron nan ya komo cikinsa.”
22 Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo.
23 Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga soro, ya kai shi cikin gida, ya ba uwar. Ya ce mata, “Ki gani, ɗanki yana da rai.”
24 Sai macen ta ce wa Iliya, “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuwa yana magana ta wurinka.”