11 Mulki yā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
12 Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi.
13 Ita da take a Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma, ɗana, Markus.
14 Ku gai da juna da sumbar ƙauna.Salama tă tabbata a gare ku duka, ku na Almasihu.