1 Daga Bulus, manzo kirayayye na Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Sastanisu,
2 zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.
3 Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
4 Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu,