3 Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu,
4 duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.
5 Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.
6 To, ai, waɗannan abubuwa gargaɗi ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.
7 Kada fa ku zama matsafa kamar yadda waɗansunsu suke. A rubuce yake cewa, “Jama'a sun zauna garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta rawa.”
8 Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak.
9 Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su.