1 A yanzu kuma, 'yan'uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi,
2 wadda kuma ake cetonku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama sama ne kuka gaskata ba.
3 Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,
4 cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa,
5 ya kuma bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun.
6 Sa'an nan ya bayyana ga 'yan'uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda, yawancinsu kuwa suna nan har zuwa yanzu, amma waɗansu sun yi barci.
7 Sa'an nan ya bayyana ga Yakubu, sa'an nan ga dukan manzanni.