1 To, a yanzu kuma ga zancen ba da gudunmawa ga tsarkaka, kamar yadda na umarci ikilisiyoyin Galatiya, haka ku ma za ku yi.
2 A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna, a tara gudunmawa.
3 Sa'ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai taimakonku Urushalima.
4 In ya kyautu ni ma in tafi, to, sai su raka ni.
5 Zan zo gare ku bayan na zazzaga ƙasar Makidoniya, don kuwa ta Makidoniya zan bi.
6 Watakila zan jima a wurinku, ko ma in ci damina, don ku yi mini rakiya duk in da za ni.
7 Ba sona ne in gan ku a yanzu in wuce kawai ba, a'a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki a wurinku, in Ubangiji ya yarda.