5 Zan zo gare ku bayan na zazzaga ƙasar Makidoniya, don kuwa ta Makidoniya zan bi.
6 Watakila zan jima a wurinku, ko ma in ci damina, don ku yi mini rakiya duk in da za ni.
7 Ba sona ne in gan ku a yanzu in wuce kawai ba, a'a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki a wurinku, in Ubangiji ya yarda.
8 Amma zan dakata a Afisa har ranar Fentikos.
9 Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.
10 In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
11 Kada fa kowa yă raina shi. Ku raka shi lafiya, ya komo a gare ni, domin ina duban hanyarsa tare da 'yan'uwa.