1 In waninku yana da wata ƙara a game da ɗan'uwansa, ashe, zai yi ƙurun kai maganar a gaban marasa adalci, ba a gaban tsarkaka ba?
2 Ashe, ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari'a? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari'a, ashe, ba za ku iya shari'ar ƙananan al'amura ba?
3 Ba ku sani ba, za mu yi wa mala'iku shari'a, balle al'amuran da suka shafi zaman duniyar nan?
4 In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, don me kuma kuke kai su gaban waɗanda su ba kome ba ne, a game da Ikkilisiya?
5 Na faɗi wannan ne don ku kunyata. Ashe, wato, ba ko mutum ɗaya mai hikima a cikinku, da zai iya sasanta tsakanin 'yan'uwa?