7 Da ma a ce kowa kamar ni yake mana! Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa, wani iri kaza, wani kuma iri kaza.
8 Abin da na gani ga waɗanda ba su yi aure ba, da kuma mata gwauraye, ya kyautu a gare su su zauna ba aure kamar yadda nake.
9 In kuwa ba za su iya kamewa ba, to, sai su yi aure. Ai, gwamma dai a yi aure da sha'awa ta ci rai.
10 Masu aure kuwa ina yi musu umarni, ba kuwa ni ba, Ubangiji ne, cewa kada mace ta rabu da mijinta
11 (in kuwa ta rabu da shi, sai ta zauna haka ba aure, ko kuwa ta sāke shiryawa da mijinta), miji kuma kada ya saki matarsa.
12 Ga sauran, ni nake faɗa, ba Ubangiji ba, in wani ɗan'uwa yana da mace marar ba da gaskiya, ta kuma yarda su zauna tare, to, kada yă rabu da ita.
13 Mace kuma mai miji marar ba da gaskiya, ya kuwa yarda su zauna tare, to, kada ta rabu da shi.