1 Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah uba da Ubangiji Yesu Almasihu.Alheri da salama su tabbata a gare ku.
2 A kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku a cikin addu'armu,
3 ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.
4 Domin mun sani, 'yan'uwa, ƙaunatattu na Allah, shi ya zaɓe ku,