1 Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ba lalle sai an rubuto muku kome ba.
2 Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.
3 Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.
4 Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, 'yan'uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo.
5 Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.
6 Ashe, saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa.
7 Don masu barci da daddare suke barci, masu sha su bugu ma da daddare suke sha su bugu.