23 Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
24 Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.
25 Ya ku 'yan'uwa, ku yi mana addu'a.
26 Ku gai da dukkan 'yan'uwa da tsattsarkar sumba.
27 Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan 'yan'uwa wasiƙar nan.
28 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.