1 Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu'a, ana godo, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane,
2 da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan maƙamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.
3 Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu,
4 wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.
5 Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum,
6 wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa.