1 Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.
2 Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
3 Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.
4 Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne.