1 Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.
2 Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu Ubangijinmu
3 Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa,
4 waɗanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi'arsa, da yake kun tsira daga ɓācin nan dake a duniya da muguwar sha'awa take haifa.
5 Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata,