3 Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa,
4 waɗanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi'arsa, da yake kun tsira daga ɓācin nan dake a duniya da muguwar sha'awa take haifa.
5 Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata,
6 sanin ya kamata da kamunkai, kamunkai da jimiri, jimiri da bin Allah,
7 bin Allah da son 'yan'uwa, son 'yan'uwa kuma da ƙauna.
8 In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
9 Domin duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance an tsarkake shi daga zunubansa na dā.