2 Ina so ku tuna da yin faɗin annabawa tsarkaka, da kuma umarnin Ubangiji Mai Ceto ta bakin manzannin da suka zo muku.
3 Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba'a za su zo suna ba'a, suna biye wa muguwar sha'awarsu,
4 suna cewa, “To, ina alkawarin dawowarsa? Ai, tun a lokacin da kakannin kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.”
5 Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa.
6 Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka.
7 Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari'a, a hallaka su.
8 Amma ya ku ƙaunatattuna kada ku goce wa magana gudar nan, cewa ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekara dubu ne, shekara dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.