4 Saboda haka, mu kanmu ma taƙama muke yi da ku a cikin ikilisiyoyin Allah, saboda jimirinku, da bangaskiyarku a cikin yawan tsananin da kuke sha, da ƙuncin da kuke a ciki.
5 Wannan kuwa ita ce tabbatar hukunci mai adalci na Allah, domin a lasafta ku a cikin waɗanda suka cancanci zama a Mulkin Allah, wanda kuke shan wuya dominsa,
6 domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku,
7 yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,
8 yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.
9 Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa,
10 wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.