2 Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zagezage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka,
3 da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta,
4 da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah,
5 suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.
6 A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha'awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali,
7 kullum suna koyo, amma kullum sai su kāsa kaiwa ga sanin gaskiya.
8 Kamar yadda Yanisu da Yambirisu suka tayar wa Musa, haka mutanen nan kuma suke tayar wa gaskiya, mutane ne masu ɓataccen hankali ƙwarai, bangaskiyarsu kuwa ta banza ce.