19 Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras.
20 Aratas ya dakata a Koranti. Tarofimas kuwa na bar shi a Militas, ba shi da lafiya.
21 Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan 'yan'uwa.
22 Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.