1 Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.
2 Ya ƙaunataccena, ina addu'a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya.
3 Na yi farin ciki ƙwarai sa'ad da waɗansu 'yan'uwa suka zo suka shaida gaskiyarka, yadda hakika kake bin gaskiya.
4 Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji 'ya'yana suna bin gaskiya.
5 Ya ƙaunataccena, duk abin da kake yi wa 'yan'uwa, aikin bangaskiya kake yi, tun ba ma ga baƙi ba.
6 Su ne suka shaida ƙaunarka a gaban ikkilisiya. Zai kyautu ka raka su a guzuri, kamar yadda ya cancanci bautar Allah,