11 Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.
12 Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa, har gaskiya kanta ma tana yi masa shaida. Mu ma mun shaide shi, ka kuwa san shaidarmu tabbatacciya ce.
13 Dā kam, ina da abin da zan rubuto maka da yawa, amma yanzu na gwammace kada in rubuto a wasiƙa.
14 Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.
15 Salama tă tabbata gare ku. Aminanmu suna gaishe ka. Ka gai da aminanmu kowa da kowa.