3 Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,
4 domin kuwa ya zaɓe mu a cikin Almasihu tun ba a halicci duniya ba, mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa.
5 Ya ƙaddara mu mu zama 'ya'yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri,
6 domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.
7 Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,
8 wanda ya falala mana. Da matuƙar hikima da basira
9 ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu.