3 Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.
4 Amma Allah da yake mai yalwar jinƙai ne, saboda matsananciyar ƙaunar da yake yi mana,
5 ko a sa'ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku),
6 a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya.
7 Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu.
8 Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah,
9 ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.