3 Da ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar da Ruhu yake zartarwa, kuna a haɗe a cikin salama.
4 Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan.
5 Ubangiji guda ne, bangaskiya guda, da kuma baftisma guda.
6 Allah ɗaya ne, Ubanmu duka, wanda yake bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.
7 Amma an ba kowannenmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu.
8 Saboda haka, Nassi ya ce,“Sa'ad da ya hau Sama ya bi da rundunar kamammu,Ya kuma yi wa 'yan adam baye-baye.”
9 (Wato, da aka ce “ya hau” ɗin, me aka fahimta, in ba cewa dā ya sauka a can ƙasa ba?