1 Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai.
2 Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,
3 don al'amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
4 Ku ubanni, kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.