10 Yunwa ta kama shi, har ya so ya ci wani abu. Ana cikin shirya abincin, sai wahayi ya zo masa,
11 ya ga sama ta dare, wani abu kuma yana saukowa kamar babban mayafi, ana zuro shi ƙasa ta kusurwoyinsa huɗu.
12 Cikinsa akwai kowace irin dabba, da masu jan ciki, da tsuntsaye.
13 Sai ya ji wata murya ta ce masa, “Bitrus, tashi, ka yanka ka ci.”
14 Amma Bitrus ya ce, “A'a, ya Ubangiji, don ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta ba.”
15 Sai ya sāke jin murya, ji na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.”
16 Da an yi wannan sau uku, nan da nan aka yi sama da abin.