1 To, manzanni da 'yan'uwan da suke a ƙasar Yahudiya suka ji, cewa al'ummai ma sun yi na'am da Maganar Allah.
2 Da Bitrus ya zo Urushalima, 'yan ɗariƙar masu kaciyar nan suka yi masa sūka,
3 suka ce, “Ga shi, ka shiga wurin marasa kaciya, har ka ci abinci tare da su!”
4 Sai Bitrus ya fara, yana yi musu bayani bi da bi cewa,