11 Da Bitrus ya koma cikin hankalinsa, ya ce, “Yanzu kam na tabbata, Ubangiji ne ya aiko mala'ikansa, ya cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”
12 Da ya gane haka, ya je gidan Maryamu, uwar Yahaya wanda ake kira Markus, inda aka taru da yawa, ana addu'a.
13 Da ya ƙwanƙwasa ƙofar zauren, wata baranya mai suna Roda ta zo ji ko wane ne.
14 Da ta shaida muryar Bitrus, ba ta buɗe ƙofar ba don murna, sai ta koma ciki a guje, ta ce Bitrus na tsaye a ƙofar zaure.
15 Sai suka ce mata, “Ke dai akwai ruɗaɗɗiya.” Ita kuwa ta nace a kan shi ne. Su kuwa suka ce, “To, mala'ikansa ne!”
16 Bitrus dai ya yi ƙwanƙwasawa, da suka buɗe suka gan shi, suka yi ta al'ajabi.
17 Shi kuwa ya ɗaga musu hannu su yi shiru, ya kuma bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakubu da 'yan'uwa waɗannan abubuwa.” Sa'an nan ya tashi ya tafi wani wuri.