24 Kafin ya bayyana a fili kuwa, Yahaya ya yi wa duk jama'ar Isra'ila wa'azi su tuba a kuma yi musu baftisma.
25 Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’
26 “Ya ku 'yan'uwa, zuriyar Ibrahim, da kuma sauran masu tsoron Allah a cikinku, mu fa aka aiko wa kalmar ceton nan.
27 Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa'an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi.
28 Ko da yake ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi.
29 Da suka cikasa dukkan abin da aka rubuta game da shi, suka sauko da shi daga kan gungumen, suka sa shi a kabari.
30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.