27 Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa'an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi.
28 Ko da yake ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi.
29 Da suka cikasa dukkan abin da aka rubuta game da shi, suka sauko da shi daga kan gungumen, suka sa shi a kabari.
30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31 Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushalima daga Galili, waɗanda a yanzu su ne shaidunsa ga jama'a.
32 Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,
33 ya cika mana shi, mu zuriyarsu, da ya ta da Yesu daga matattu, yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,‘Kai Ɗana ne,Ni Ubanka ne yau.’