34 Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi, a kan cewa ba zai sāke komawa cikin halin ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce,‘Zan yi muku tsattsarkar albarkar nan da na tabbatar wa Dawuda.’
35 Domin a wata Zabura ma ya ce,‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
36 Dawuda kam, bayan da ya bauta wa mutanen zamaninsa bisa ga nufin Allah, ya yi barci, aka binne shi tare da kakanninsa, ya kuwa ruɓe.
37 Amma shi wannan da Allah ya tashe shi, bai ruɓa ba.
38 Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.
39 Ta gare shi kuma, duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukan abubuwan da ba dama Shari'ar Musa ta kuɓutar da ku.
40 Saboda haka sai ku mai da hankali, kada abin nan da littattafan annabawa suke faɗa ya aukar muku, wato