4 Su kuwa, da Ruhu Mai Tsarki ya aike su, suka tafi Salukiya, daga can kuma suka shiga jirgin ruwa sai tsibirin Kubrus.
5 Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami'un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu.
6 Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafusa, suka iske wani mai sihiri, annabin ƙarya, Bayahude, mai suna Bar-yashu'a,
7 Wanda yake tare da muƙaddas Sarjiyas Bulus, mutum mai basira. Sai muƙaddashin ya kira Barnaba da Shawulu ya nemi jin Maganar Allah.
8 Amma Alimas mai sihirin nan, (don wannan ita ce ma'anar sunansa), ya mūsa musu, yana neman bauɗar da muƙaddashin nan daga bangaskiya.
9 Shawulu kuwa, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba masa ido,
10 ya ce, “Kai babban maha'inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?