1 To, a Ikoniya suka shiga majami'ar Yahudawa tare, suka yi wa'azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da al'ummai, suka ba da gaskiya.
2 Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al'ummai, suka ɓata tsakaninsu da 'yan'uwa.
3 Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa'azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi ta hannunsu.
4 Amma mutanen birni suka rarrabu, waɗansu suka koma bayan Yahudawa, waɗansu kuma bayan manzannin.
5 Sa'ad da al'ummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasar wa manzannin, su wulakanta su, su jejjefe su da duwatsu,
6 suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya wato Listira da Darba, da kuma kewayensu.