8 Suka kuwa ratsa ƙasar Misiya, suka gangara zuwa Taruwasa.
9 Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”
10 Da kuwa ya ga wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu bishara.
11 Shi ke nan fa, sai muka tashi a jirgin ruwa daga Taruwasa, muka miƙe sosai har zuwa tsibirin Samutaraki, kashegari kuma sai Niyabolis,
12 daga nan kuma sai Filibi ta ƙasar Makidoniya, wadda take babbar alkarya ce a wannan waje, birnin Romawa ne kuma. A nan birnin muka yi 'yan kwanaki.
13 Ran Asabar muka fita ƙofar gari, muka je bakin kogi, inda muke tsammani akwai wurin yin addu'a. Nan muka zauna, muka yi wa matan da suka taru magana.
14 Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.