5 Amma Yahudawa, saboda kishi, suka ɗibi waɗansu ashararai, 'yan iska, suka tara jama'a suka hargitsa garin kaf, suka fāɗa wa gidan Yason, suna nemansu don su fito da su gaban taron jama'a.
6 Da ba su same su ba, suka jawo Yason da waɗansu 'yan'uwa, har gaban mahukuntan garin, suna ihu suna cewa, “Mutanen nan masu ta da duniya a tsaye, ga su sun zo nan ma,
7 har ma Yason ya sauke su! Dukansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wani ne sarki, wai shi Yesu.”
8 Da mutanen gari da mahukunta suka ji wannan, hankalinsu ya tashi.
9 Ba su sake su ba, sai da suka karɓi kuɗin lamuni a hannun Yason da sauransu.
10 Nan da nan kuwa da dare ya yi, 'yan'uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Biriya. Da suka isa can kuma suka shiga majami'ar Yahudawa.
11 To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.