1 To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi,
2 sai ya ce musu, “Kun sami Ruhu Mai Tsarki sa'ad da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma ji zuwan Ruhu Mai Tsarki ba.”
3 Sai ya ce, “To, wace baftisma ke nan aka yi muku?” Suka ce, “Irin ta Yahaya ce.”
4 Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.”
5 Da suka ji haka, aka yi musu baftisma da sunan Ubangiji Yesu.
6 Da Bulus ya ɗora musu hannu, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, suka kuwa yi magana da waɗansu harsuna, suna annabci.
7 Su wajen sha biyu ne duka duka.