16 Mutumin nan mai aljanin sai ya daka tsalle, ya fāɗa musu, ya fi ƙarfinsu dukkansu, ya ci ɗunguminsu, har suka fita daga gidan a guje, a tuɓe, suna masu rauni.
17 Wannan abu fa ya sanu ga dukan mazaunan Afisa, Yahudawa da al'ummai duka, duka kuma tsoro ya kama su, aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu.
18 Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu a fili.
19 Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone a gaban jama'a duka. Da suka yi wa littattafan nan kima, sai suka ga sun kai kuɗi azurfa dubu hamsin.
20 Sai kuma Maganar Ubangiji ta ƙara haɓaka, ta kuma fifita ƙwarai.
21 Bayan waɗannan al'amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”
22 Da ya aiki mataimakansa biyu Makidoniya, wato Timoti da Arastas, shi kuwa ya ɗan dakata a ƙasar Asiya.