11 da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manyan al'amuran Allah da bakunan garuruwanmu.”
12 Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?”
13 Amma waɗansu suka yi ba'a suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka yi tatul!”
14 Amma Bitrus ya miƙe tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku 'yan'uwana Yahudawa da dukan mazaunan Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata.
15 Ai, mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda kuke zato, tun da yake yanzu ƙarfe tare na safe ne kawai.
16 Wannan, ai, shi ne abin da Annabi Yowel ya faɗa cewa,
17 ‘Allah ya ce,A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan 'yan adam Ruhuna.'Ya'yanku mata da maza za su yi annabci,Wahayi zai zo wa samarinku,Dattawanku kuma za su yi mafarkai.