4 Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.
5 To, a Urushalima a lokacin, akwai waɗansu Yahudawa masu bautar Allah daga ko'ina cikin ƙasashen duniya.
6 Da jin dirin nan kuwa, taron ya haɗe, ya ruɗe, domin ko wannensu ya ji suna magana da bakin garinsu.
7 Sai suka yi al'ajabi suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne?
8 Ƙaƙa kuwa ko wannenmu yake ji da bakin garinsu ake magana?
9 Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,
10 da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci,