1 Bayan hargowar nan ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.
2 Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa masu zuciya ƙwarai, ya zo ƙasar Hellas,
3 ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa'ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.
4 Subataras Babiriye, ɗan Burus, shi ya raka shi, tare da Aristarkus da Sakundas, mutanen Tasalonika, da Gayus Badarbe, da Timoti, har ma da Tikikus da Tarofimas, mutanen Asiya,
5 waɗanda suka riga tafiya suka jira mu a Taruwasa.