16 To, a yanzu me kake jira? Tashi, a yi maka baftisma a wanke zunubanka ta wurin kira bisa sunansa.’ ”
17 “Da na komo Urushalima, ina addu'a a Haikali, sai wahayi ya zo mini.
18 Na gan shi, yana ce mini, ‘Yi sauri maza ka fita daga Urushalima, don ba za su yarda da shaidarka a kaina ba.’
19 Ni kuma na ce, ‘Ya Ubangiji, ai, su ma kansu sun sani a kowace majami'a na ɗaɗɗaure waɗanda suka gaskata da kai, na kuma daddoke su.
20 Sa'ad da kuma aka zub da jinin Istifanas, mashaidin nan naka, ni ma ina a tsaye a gun, ina goyon bayan abin da aka yi, har ma ina tsare tufafin masu kisansa.’
21 Sai ya ce mini, ‘Tashi ka tafi, zan aike ka can nesa a wurin al'ummai.’ ”
22 Suna ta sauraronsa har ya iso kalmar nan, sai suka ɗau ihu suka ce, “A kashe shi! A raba irin mutumin nan da duniya, bai kyautu ya rayu ba!”