1 Bayan kwana biyar sai babban firist, Hananiya, ya zo tare da waɗansu shugabanni, da kuma wani lauya, mai suna Tartulus, suka yi ƙarar Bulus a gaban mai mulki.
2 Da aka kirawo Tartulus, ya shiga kai ƙarar Bulus, ya ce, “Ya mafifici Filikus, tun da yake ta gare ka ne muke zaman lafiya ƙwarai, ta tsinkayarka ne kuma ake kyautata zaman jama'armu,
3 kullum muna yarda da haka ƙwarai a ko'ina, tare da godiya ba iyaka.
4 Amma don kada in gajiyad da kai, ina roƙonka a cikin nasiharka, ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.