16 Saboda haka, a kullum nake himma in kasance da lamiri marar abin zargi a wurin Allah da wurin mutane.
17 To, bayan 'yan shekaru sai na je domin in kai gudunmawa ga jama'armu, in kuma yi sadaka.
18 Ina cikin yin haka sai suka same ni a tsarkake a Haikali, ba kuwa da wani taro ba, balle hargowa. Amma akwai waɗansu Yahudawa daga ƙasar Asiya–
19 su ne kuwa ya kamata su zo nan a gabanka su yi ƙarata, in suna da wata magana a game da ni.
20 Ko kuwa waɗannan mutane kansu su faɗi laifina da suka samu, sa'ad da na tsaya a gaban majalisa,
21 sai ko maganar nan ɗaya tak, da na ɗaga murya na faɗa, sa'ad da nake a tsaye a cikinsu, cewa, ‘Game da maganar tashin matattu ake yi mini shari'a a gabanku yau.’ ”
22 Filikus kuwa da yake yana da sahihin ilimi a game da wannan hanya ya dakatar da su, ya ce, “In shugaba Lisiyas ya iso, zan yanke muku shari'a.”