10 ya ce musu, “Ya ku jama'a, na dai ga tafiyar nan za ta zamanto da masifa da hasara mai yawa, ba wai ta kaya da jirgi kawai ba, har ma ta rayukanmu.”
11 Amma jarumin soja, ya fi mai da hankali ga maganar mai tuƙin jirgin da kuma ta mai jirgin, a kan abin da Bulus ya faɗa.
12 Da yake mafakar nan ba ta kamaci jirage su ci damuna a ciki ba, sai yawanci suka kawo shawara a tashi daga nan, ko ta ƙaƙa su iya kaiwa Finikiya, wata mafakar tsibirin Karita, mai duban gabas maso arewa da kuma gabas maso kudu, su ci damuna a can.
13 Da iska ta buso daga kudu sannu sannu, a tsammaninsu muradinsu ya biya ke nan, sai suka janye anka suka bi ta gefen tsibirin Karita gab da gaci.
14 Ba da jimawa ba kuwa sai ga wata gawurtacciyar iska da ake kira Yurokilidon ta bugo daga tsibirin.
15 Da iskar ta bugo jirgin, har ya kasa fuskantarta, sai muka sallama mata, ta yi ta kora mu.
16 Da muka bi ta jikin wani ɗan tsibiri wai shi Kauda muka samu muka yi iko da ƙaramin jirginmu da ƙyar.