1 Bayan da muka tsira, sai muka ji, ashe, sunan tsibirin nan Malita ne.
2 Mutanen garin kuwa sun yi mana alheri matuƙar alheri, don sun hura wuta sun karɓe mu, mu duka, saboda ana ruwa, ga kuma sanyi.
3 Sa'ad da Bulus ya tattaro waɗansu ƙirare rungume guda ya sa a wutar, sai ga wani maciji ya bullo saboda zafi, ya ɗafe masa a hannu.
4 Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”
5 Bulus kuwa ya karkaɗe ƙwaron a cikin wutar, bai kuwa ji wani ciwo ba.