9 Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkar da su.
10 Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da muke bukata.
11 Bayan wata uku muka tashi a cikin wani jirgin Iskandariya, wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwaye Maza.
12 Da muka zo Sirakusa muka kwana uku a nan.
13 Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana, iska ta taso daga kudu, kashegari kuma muka kai Butiyoli.
14 A nan muka tarar da waɗansu 'yan'uwa, suka roƙe mu mu kwana bakwai tare da su. Da haka dai har muka isa Roma.
15 Da 'yan'uwa na can suka ji labarinmu, sai da suka zo don su tarye mu har Kasuwar Abiyus, da kuma wurin nan da ake kira Maciya Uku. Da kuwa Bulus ya sadu da su, ya yi godiya ga Allah, jikinsa kuma ya yi ƙarfi.