13 Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi, a gaban Bilatus, sa'ad da ya ƙudura zai sake shi.
14 Amma ku kuka ƙi Mai Tsarkin nan, mai adalci kuka roƙa a saukar muku da mai kisankai,
15 kuka kuwa kashe Tushen Rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga haka.
16 To, sunansa ne, wato ta wurin bangaskiya ga sunansa, shi ne ya ba mutumin nan da kuke gani, kuka kuma sani, ƙarfi. Hakika, bangaskiyar da take ta wurin Yesu ita ta ba mutumin nan cikakkiyar lafiya, a gaban idonku duka.
17 “To, yanzu 'yan'uwa, na sani da jahilci kuka yi haka, kamar yadda shugabanninku ma suka yi.
18 Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa Almasihunsa zai sha wuya.
19 Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,